Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli a Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Sa’ad Abubakar na uku, ya yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadago da su janye batun yajin aiki da zasu shiga a faɗin ƙasar daga ranar Talata 3 ga watan Oktoba.
Sarkin ya bayyana hakan ne a wajen bude taron shirya bikin cikar ƙasar nan shekaru 63 da samun ‘yancin kai wanda ya gudana a jiya Juma’a a birnin tarayya Abuja.
Ya jaddada buƙatar tattaunawa don nemo mafita kan batutuwan maimakon fara yajin aikin ko don maslahar talakawa.
A ƙarshe ya ce yana mai bayar da shawarar tattaunawa ne saboda yajin aikin ba zai magance matsalolin ƙasar nan ba.