Home » Fitar da zakka zai kawo karshen talauci a Najeriya ~ Nuruddeen Muhajid

Fitar da zakka zai kawo karshen talauci a Najeriya ~ Nuruddeen Muhajid

by Anas Dansalma
0 comment
Fitar da zakka zai kawo karshen talauci a Najeriya ~ Nuruddeen Muhajid

Gidauniyar Zakka da Wakafi ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa, fitar da zakka da kuma bayar da ita ga wadanda addini yace a bai wa sune kadai za su iya magance tsananin talaucin dake addabar jama’a.

Sakataren gidauniyar Zakka da Wakafi ta Jihar Kaduna, Malam Nuruddeen Muhajid ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai.

Muhajid ya kara da cewa bisa la’akari da halin da jama’ar Musulmi suka tsinci kansu a ciki na yin sakaci da wannan rukuni na bayar da Zakka ne ya sa suka samar da wannan gidauniya wadda take tattara Zakka gami da rarraba ta ga al’umma kuma ita ce ta farko irinta a Jihar Kaduna.

Sakataren ya kara da cewa sun kafa gidauniyarsu ne tun a shekarar 2021, kuma tun daga wannan lokaci suke aikin tara kudaden Zakka daga hannun masu hannu da shuni.

A cewarsa, a shekarar farko sun raba naira miliyan Uku, sannan a shekara ta biyu suka raba naira miliyan 10, yayin da a shekarar bara suka raba naira miliyan 16.

Ya ce a farkon shekarar nan sun gudanar da babban taro na kasa domin wayar da kan jama’a a kan muhimmancin bayar da Zakka. Inda suka gayyaci jama’a daga dukkanin jihohin kasar nan 36 har da Abuja aka yi babban taro a  Kaduna wanda kuma an samu nasara sosai.

Ya bukaci daukacin al’ummar Jihar Kaduna musamman masu hannu da shuni da su rika fitar da Zakka domin rage radadin talauci da ya yi wa al’umma katutu. Ya ce kofar gidauniyarsu a bude take wajen amsar Zakka da Wakafi domin raba su ga wadanda suka dace .

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi