A dai dai lokacin da ake tsaka da gudanar da bukukuwan babbar Sallah Mai alfarma Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwar nisabin Zakkah, da Sadaki da Diyyar rai.
A sanarwar da sarkin Musulmin ya fitar, wacce hukumar kula da ganin jinjirin wata ta yada a shafinta na Facebook ta ce, yanzu nisabin Zakkah ya koma naira miliyan 3 da dubu dari 918 da dari 800…… (N3,918,800,)
Sai Diyyar rai wanda kudin ya kama naira miliyan N195 da dubu 940,000, duba da darajar kudade da ake dasu a yanzu.
A bangaren haddin sata da sadakin aure kuwa, mafi ƙaranci shine N48,985.
Wannan kaɗan kenan daga cikin hanyoyin da addinin Islama ya tanada don yiwa kowa adalci a fannin gudanar da rayuwar yau da kullum.