Home » Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin shugaban kasar Guinea-Bissau kuma shugaban ECOWAS

Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin shugaban kasar Guinea-Bissau kuma shugaban ECOWAS

by Anas Dansalma
0 comment
Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin shugaban kasar Guinea-Bissau kuma shugaban ECOWAS

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce babban burinsa shi ne ya sake mayar da kasar nan jagora a kan sauran kasashen Afirka.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Umaro Sissoco Embaló, shugaban kasar Guinea-Bissau, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ECOWAS.

Shugaba Tunubu ya ce ya ji dadin karbar bakuncin Umaro Sissoco yana mai cewa sun ci abinci tare kuma sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafe su.

Ya kuma ƙara da cewar, a yayin da wannan gwamnati take faman ganin ta maido da Nijeriya a matsayin jagora a Afirka, yana sa ran samun hadin-kai da dangantaka mai armashi da dukkan kasashen da ke yankin afrika.

A lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, Shugaba Tinubu ya sha alwashin kyautata dangantaka tsakanin Nijeriya da kasashen Afirka.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi