Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga masarautun gargajiya a Najeriya da su riƙa rubuta tare da adana tarihinsu, domin ka da wasu mutane su rubuta tarihin da bai tabbata ba.
Sarkin Musulmin ya yi wannan magana ne ranar Laraba a Zariya, yayin bikin ƙaddamar da littafin “Emirs of Zazzau: A Biographical Study from 1800–1925”, wanda ya ƙunshi tarihin sarakunan Zazzau daga shekarar 1800 zuwa 1925.
An ƙaddamar da littafin ne a wani ɓangare na bikin cikar shekaru shida da zama Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.
Sarkin Musulmi ya yaba wa Sarkin Zazzau kan ƙoƙarin rubuta tarihin masarautar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kare tarihi, al’adu da asalin al’ummar Zazzau.
Ya ce masarautu su ne suka fi cancanta su rubuta tarihinsu saboda su ne suka fi sanin abubuwan da suka faru a kansu.
“Ba za ku bari wani ya rubuta tarihinku ba. Dole ne ku rubuta tarihinku yadda yake, domin kun fi kowa saninsa,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa a baya ya buƙaci Sarkin Zazzau ya yi koyi da yadda aka rubuta tarihin Daular Sakkwato, inda ya ce shi ma ya wallafa littafin “Sultans of Sokoto” shekaru da dama da suka gabata.
A cewarsa, littafin tarihin Zazzau ya kasance na musamman saboda masana tarihi daga manyan dauloli guda huɗu na masarautar sun taimaka wajen samar da shi.
Sarkin Musulmin ya kuma buƙaci sauran masarautu a Najeriya da su yi irin wannan aiki domin adana tarihinsu yanzu da kuma waɗanda za su zo nan gaba.
Ya ce ya kamata mutane su san tarihinsu, inda suka fito da kuma inda suke son zuwa.
“Dole mu san su waye mu, daga ina muka fito da kuma inda za mu dosa. Ka da mu bari kafafen sada zumunta su rubuta duk abin da suke so, su kuma sauya tarihinmu,” in ji shi.
Sarkin Musulmin ya kuma gargaɗi al’umma kan dogaro da wasu bayanan tarihi da mutanen da ba su da cikakken sani kan tarihin da al’adun Najeriya suka rubuta.
Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabannin ƙasar addu’a, ciki har da gwamnonin jihohi, sarakuna da sauran shugabannin gargajiya da na siyasa.
Ya ce nasarar shugabanni za ta amfani al’ummar da suke jagoranta.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yaba wa Sarkin Zazzau kan ƙoƙarin rubuta tarihin masarautar.
Ya ce littafin zai taimaka wajen adana muhimman bayanai game da tarihin Zazzau.
Gwamnan ya shawarci Sarkin Zazzau da ya ci gaba da haƙuri, sauraron jama’a da kuma amfani da shawarwari masu amfani wajen tafiyar da masarautar.
Ya kuma gode wa Sarkin Musulmi bisa goyon bayan da yake bai wa Masarautar Zazzau da kuma halartar bikin cikar shekaru shida da hawan Sarkin Zazzau.
Shi ma Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce wallafa littafin ya zama dole saboda an samu kura-kurai da wasu bayanai da ba su inganta ba a tarihin Zazzau.
Ya ce al’ummar da ba ta rubuta tare da adana tarihinta ba tana cikin hatsarin rasa asali, al’adu da kuma alaƙar da ke tsakaninta da al’ummar da za su zo nan gaba.
Sarkin ya gode wa manyan baƙi da suka halarci bikin, tare da yin kira a haɗa kai a tsakanin masarautu domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’umma.
Taron ya samu halartar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, masana tarihi, mambobin Majalisar Masarautar Zazzau da sauran manyan baƙi.