Sen. Barau Jibrin Ya Shiga Sahun Masu Zawarcin Shugabancin Majalisar Dattawa

Sanata Barau Jibrin ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban majalisar dattawa a majalisa ta 10.

Sanarwar tasa na zuwa ne jum kaɗan bayan da babban mai tsawatarwar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce lokaci ya yi da zai zama shugaban majalisar dattawa.

Da yake zantawa da manema labarai a zauren majalisar, Sanata Barau ya ce cancanta da iya aiki da gogewa su ya kamata su zama abubuwan da za su iya tantance wanda ya kamata ya zama shugaban majalisar dattawa a majalisa ta 10.

Sai dai ya ce bai kamata a yi amfani da Addini wajen samar da shugaban majalisar ba.

A cewarsa, bai kamata ra’ayin addini ya zama sanadin tantance wanda zai jagoranci majalisar ta 10 ba.

Gwagwarmayar neman mukaman manyan jagororin majalisar ta 10 na kara zafafa ganin yadda wasu zababbun ‘yan majalisar tarayya da aka zaba a majalisar dattawa suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takara, kuma rahotanni sun bayyana cewa suna zawarcin abokan aikinsu domin neman goyon baya.

Sauran zababbun Sanatoci da suka nuna sha’awarsu na zama Shugaban Majalisar Dattawa sun hada da Godswill Akpabio da David Umahi.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere