Kungiyar Sa-Ido Kan Harkokin Tattalin Arziki (SERAP), ta yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa da ta binciki wasu gwamnonin Jihohi da mataimakansu kan zargin bangar siyasa da siyan kuri’u a zaben 2023 da aka kammala.
SERAP ta yi wannan kiran ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, inda ta bukaci hukumar zaɓen da wani kwamitin shari’a mai zaman kansa da su binciki zargin tashe-tashen hankula da sauran laifukan karya dokar zabe da ake zargin wasu masu rike da mukaman siyasa da yi a ƙasar nan.
Kungiyar ta yin barazanar gurfanar da hukumar zabe gaban kotu idan har ba ta binciki wadanda ake zargi da aikata laifuka da masu daukar nauyinsu da suka aikata miyagun laifuka a lokacin zaben ba, kuma dole ne a gurfanar da kowaye a gaban kuliya tare da hukunta shi.