Ajuri Ngelale ya zama mai ba wa shugaba Tinubu shawara na musamman kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nadin Ajuri Ngelale a matsayin mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a kuma mai magana da yawunsa.

Kamar yadda wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta nakalto, nadin na Ajuri ya fara aiki ne nan take daga ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata.

Tinubu ya bukaci sabon mai magana da yawun nasa da ya yi amfani da kwarewa da gogewarsa wajen gudanar da aikin da ke gabansa a halin yanzu.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan wannan nadin, Ngelale ya ce, ya yi matukar farin ciki da annashuwa bisa zabin da shugaban ya yi masa, tare da shan alwashin zai yi aiki tukuru domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr