Babban Sakataren Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya Abuja, Malam Shehu Ahmed, ya ce hukumar za ta rusa dukkan gine-ginen da ke kan hanyoyin magudanan ruwa a fadin garin na Abuja.
Ahmed ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi a Abuja.
Ya ce wasu gine-ginen na hana ruwa gudu ta hanyar da ta dace wanda ke haddasa ambaliya da aka samu a wasu sassan birnin.
Sakataren ya ce, Mutane suna ta korafin cewa su yi gaggawar daukar matakai don ceto rayuka daga hatsarin da ke tattara da wannan karya tsarin birnin na Abuja.
Ya kuma ƙara da cear, sun gaya wa mazauna tiredimo (Trademore) su yi kaura, domin ƴankin yana kan hanyar ruwa, kuma ambaliyar ruwan na iya zuwa a kowane lokaci, amma sunyi biris da wannan matsalar tsawon shekaru.