Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin da zai kawo gyara ta fuskar haraji da farfado da tattalin arzikin kasar nan.
Toh sai dai abin da ya fi daukar hankalin mutane shi ne, ganin Orire Agbaje ta shiga cikin wannan kwamiti da ya tattara kwararru da masana.
Orire Agbaje, daliba ce da ke karatu a jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo, kuma budurwa, ta na karantar ilmin tattalin arziki ne.
Kamar yadda sanarwar fadar shugaban kasa ta fitar, Agbaje ta na aji hudu ne a jami’a, abinda ke nuna cewar a shekarar nan za ta kammala karatun digirinta na farko, dalibar ta samu damar zama kafada da kafada da masana tattalin arziki.
Rahortanni sun tabbatar da cewa, dalibar ta na cikin gidauniyar NHEF ta masana daga cikin wadanda su ke karatun gaba da sakandare.
Haka kuma, Agbaje ta na rike da shugabancin kungiyoyi biyu a wannan tsohuwar jami’a mai dinbin tarihi ta Ibadan.