Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya wuce birnin Paris na ƙasar Faransa daga birnin Landan na Birtaniya a yau Juma’a.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari ne ya bayyana hakan bayan ya kai masa ziyara a Landan.
Masari ya bayyana hakan ne a wani saƙo a shafinsa na X inda ya ce:
“Yau na yi nasarar kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ziyara a gidansa da ke Birtaniya, inda muka yi tattaunawa mai amfani,” “Daga nan kuma sai muka wuce birnin Paris na Faransa domin yin wasu ayyukan masu muhimmanci.”
- Hukumar “Immigration” Ta Yi Bikin Ƙarawa Jami’anta 450 Mukami a Kano
- Sarkin Musulmi Ya Roƙi ‘Yan Najeriya Su Cigaba Da Yiwa Shugabanni Addu’a.
Tun a ranar 2 ga watan Oktoba ne dai Tinubu ya tafi Birtaniya domin yin hutun mako biyu, kamar yadda fadarsa ta bayyana a lokacin, amma ba ta ce zai je Faransa ba.
Fadar ta ce, Tinubu zai koma gida da zarar hutun ya ƙare.