Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, zai gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya a yau, 1 ga watan Oktoba, 2023 da misalin ƙarfe 7 na safe.
Wannan sanarwa ta fito ne ta hannun mai mataimaka wa shugaban ta bangaren yaɗa labarai, Ajuri Ngelale.Ya kuma buƙaci sauran kafafen yaɗa labarai da su haɗa kai da gidan Talabijin ta ƙasa (NTA) da gidan Rediyon Najeriya domin yaɗa wannan hira da za a yi.
Wannan jawabi na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke cika shekaru sittin da uku da samun ‘yancin kai daga ƙasar Birtaniya.