Home » Shugaban mulkin soja na Nijar ya kaddamar da sabon taken kasar

Shugaban mulkin soja na Nijar ya kaddamar da sabon taken kasar

by Auwal Hussain Adam
0 comment
Shugaban mulkin soja na Nijar ya sake kaddamar da sabon taken kasar

Kasar Nigar a kokarinta na yin watsi da abin da ta gada daga mulkin-mallakar Faransa na taken kasa Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da sabon taken kasa mai nuna kima da burin ci gaban kasar ta Yammacin Afirka.

An fara amfani da sabon taken a Nijar kafin ma juyin mulkin da sojoi suka yi wa gwamnatin shugaba Mohammed Bazoum.

Sabon taken kasar da aka kaddamar a ranar 22 ga watan Yunin wannan shekarar mai suna L’Honneur de la Patrie wato Mutuncin Kasarmu ta Gado ya maye gurbin taken da dan kasar Faransa Maurice Albert Thiriet ya rubuta a shekarar 1960 mai suna La Nigérienne, wanda yake dauke da jimlolin da mafi yawan ‘yan kasar Nijar ke ganin cewa suna tunatar da zaman da kasar ta yi a karkashin mulkin-mallaka, kuma jimlolin suna fifita farar-fata a kansu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi