Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, ta ce ta kwace lasisin gudanar duk wasu ‘yan wasa da jarumai ciki har da daraktoci, gidajen gala da masu tallan maganun-uwan gargajiya a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood.
Shugaban hukumar, Abba Al-Mustapha ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne da nufin tsaftace masana’antar da kuma tabbatar da duk wanda ke ci-kin na bin ka’ida.
Al-Mustapha ya ce dole ne dukkan fitattun jarumai da furodusoshi su sabunta la-sisin yin aiki a masana’antar da hukumar tace fina-fanai ta Jihar Kano, domin kyau-tata sana’ar da kuma kauce wa gurbatattun da ke zubar da kimar sana’ar.
Sai dai kuma wannan matsayi na Al-Mustapha ya jawo suka daga mutane da da-ma, musamman ‘yan adawa wadanda suke ganin ana so a yi amfani da siyasa ne kawai domin musguna wa wasu ‘yan fim da ba su goyi bayan gwamnati mai ci ba.