Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ɗaukacin shugabannin Afrika da su mutunta ƴancin dimokuraɗiyya da doka-da-oda da kuma wanzuwar siyasa.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a taron tsakiyar shekara na gamayyar Kungiyoyin Haɗin Kan Afirka da na rassan ƙungiyoyin tattalin arzikin ƙasashen yankin Afirka da ke gudana a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.
Tinubu ya buƙaci mahukuntan ƙasashen na Afrika da su tabbatar sun mutunta batun sake sabunta mulkin dimokuraɗiyya.
Shugaban ƙasar wanda ya kasance sabon shugaban kungiyar Ecowas, ya ce ya kamata a yi watsi da batun juyin mulki a faɗin nahiyar, musamman ma wannan lokaci da ake fama da rashin tsaro da sauyin yanayi da kuma annobar korona.
Ya ce abin takaici ne ganin cewa duk da kasancewar Yammacin Afrika sahun gaba wajen ɗaɓɓaka dimokuraɗiyya da kuma kyakkyawar shugabanci, ita ke gaba a yankin wajen amfani da hanyoyi da suka saɓa wa kundin tsarin mulki don sauya gwamnati.