Jam’iyyar PDP ta buƙaci shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, farfesa Mahmood Yakubu da ya ajiye aikinsa.
Wannan batu na zuwa ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin jam’iyyar ta ƙasa, inda sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa suna Alla-wadai da saɓawa ƙunshin dokar zaɓe ta shekarar 2022 da kuma jirkita sakamakon zaɓe da jam’iyyar ke zargin shugaban hukumar zaɓen da yi.
Jam’iyyar ta bayyana fargabarta game da cigaba da zaman farfesa Mahood a matsayin shugaban hukumar zaɓen a matsayin abin da ka iya cigaba da naƙasta martabar da hukumar ke da shi da ingancin zaɓen ƙasar nan da ma martabar ƙasar kacokan a duniya.
Bisa waɗannan dalilai ne PDP ke ganin rashin cancantar Yakubun a matsayin shugaban hukumar zaɓen ta ƙasa da kuma la’akari da irin watsi da ƙarfin guiwar da al’ummar ƙasar nan ke da shi a kansa da sauran jam’iyyun siyasar ƙasar nan.
Sannan jam’iyyar ta buƙaci hukumar yaƙi da cin hanci da hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa zangon ƙasa da ta gaggauta fara bincike kan wasu jami’an hukumar da ake zargi da karɓar cin hanci domin yi wa zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar zagon ƙasa.