Jami’an rundunar tsaron haɗin gwiwa sun kuɓutar da mutum uku daga cikin biyar da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙauyen Lakwaya da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindiga sun kai sabon hari ne a garin Lakwaya da ke Gwarzo, inda suka yi awon gaba da mutane biyar.
Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Bitget na 3 na Sojin Najeriya, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya shaida wa wakilinmu cewa, “zuwa mutum uku an kubutar da su.”
Kyaftin Zubairu ya tabbatar da cewa sojoji suna yin iya ƙoƙarinsu don dawo da ragowar waɗanda aka sace cikin aminci.
A cewar majiyoyin yankin, lamarin ya faru ne da dare ranar Lahadi a ƙauyen Zurin Mahauta, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tsoro da tashin hankali.
Mai unguwar Zurin Mahauta, Murtala Mai Unguwa, ya bayyana cewa maharan sun shigo yankin cikin duhu, suka yi awon gaba da waɗanda aka sace zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Ya ce an sanar da jami’an tsaro nan take, kuma suka amsa da gaggawa, ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙari don bin diddigin masu garkuwa da mutane da kuma kuɓutar da sauran waɗanda aka sace.
Mazauna yankin sun nuna damuwa kan yawan hare-haren da ke maimaituwa a yankin, tare da yin kira da a ci gaba da samar da tsaro mai ɗorewa domin kare rayuka da dukiyoyi.
