An yanka Ladanin masallaci a Kano

Wani matashi ya yi wa wani Ladani mai Mallam Zubairu Kasim dan shekaru 70 yankan rago a wani masallaci a unguwar Maraba Hotoro  dake kano.

Al’ummar unguwar sun shiga damuwa bayan matashin da ake zargi ya yanke maƙogwaron dattijon a lokacin kiran Sallar Asubahin ranar Litinin.

An ruwaito cewa da misalin ƙarfe 5 na asuba, wanda ake zargin ya far wa Ladanin, ya rinjaye shi, ya yanka wuyansa, ya bar shi cikin jini.

Lamarin ya jawo hankalin maƙwabta, suka far wa matashin da kulake da wuƙa, amma ba su iya shawo kansa ba, ya tsere, ya shiga wani gida.

Wasu azauna unguwar sun ce matashin ya iske ladanin wasu mutane uku a masallacin, inda ya nemi a tayar da sallah, amma ladanin ya bayyana masa cewar lokaci bai ƙarasa ba.

Daga nan ya zaro wuƙa daga aljihunsa ya soka masa a maƙogwaro harma aka yi zargin ya cire maƙogoron marigayin ya sanya a leda.

Wannan ya sa ’yan unguwar suka ce da wa Allah Ya hada su in ba shi ba, amma ya suka kasa kama shi, inda ya tsere ya shiga wani gida, inda ya soka wani matashi mai shekaru 26, wanda yake barci a dakinsa wuka a fuska.

Daga karshe fusatattun mutanen unguwar suka kamo shi, suka lakaɗa masa duka, har ya ce ga garinku nan, Sun kuma far wa gidansa domin cinna masa wuta.

Yayan marigayin suna bayyana alhininsu kan faruwar lamarin, inda suka ce mahaifiin nasu mutum kirki ne  wanda baya fada da kowa.

rundunar yan sandan jihar ta bakin mai magana da yawun ta , CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce tuni al’amura suka daidaita a yankin , kuma za su ci gaba da gudanar da bincike don kamo duk wanda yake hannu kan faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *