Sojoji sun kashe ƙasurgumin ɗan ta’adda Gwaska Ɗanƙarami

Sojojin Najeriya sun halaka ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska Ɗanƙarami tare da wasu ’yan ta’adda da dama a Jihar Zamfara.

Sojojin rundunar Operation Fansan Yamma sun aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin musayar a wata maɓoyar da ’yan bindiga sama da 100 suka taru da nufin ƙaddamar da hare-hare a kama fararen hula da jami’an tsaro.

Kakakin rundunar Laftanar-Kanar Olaniyi Osoba, ya bayyana a cikin sanarwar cewa, sojojin ƙasa da jiragen yaƙi sun ragargaji ’yan ta’addan da suka yi yunƙurin tserewa a yayin farmakin na a ranar Asabar 31 ga Janairu, 2026, inda aka halaka ɓata-garin da dama, wasu kuma suka sha da ƙyar da munanan raunukan harbi.

Laftanar-Kanar Olaniyi Osoba ya ce, “Sojoji sun kone sansanin sa’annan jiragen yaƙi sojojin ƙasa ke ci gaba da sintiri domin murƙushe ragowar ’yan bindigar da suka tsere.

“Sai dai an yi rashin sa’a wasu daga cikin sojojin sun kwanta dama a yayin arangamar.”

Ya bayyana cewa rundunar za ta ci gaba sadaukar da kai tare da yin duk mai yiwuwa domin murƙushe ayyukan ’yan bindiga da hanyoyin samun kayayyakinsu a faɗin yankin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *