Dakarun Rundunar ‘Operation Haɗin Kai’ sun kashe ’yan ta’adda biyu tare da ƙwato makamai da kayan aiki a wani ƙazamin artabu da suka yi a hanyar Pulka zuwa Kirawa a Jihar Borno.
Majiyoyin soja sun bayyana cewa, a ranar Alhamis ne aka yi arangamar a yayin da sojoji suka yi artabu da wasu gungun ’yan ta’adda da ke yunƙurin tsallakawa zuwa yankin Dar-Jamal da ke kusa da Axis na Miyanti.
Rikicin da ya yi sanadin ci gaba da musayar wuta, ya kai ga halaka ’yan ta’adda biyu, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
- Rikicin Cikin Gida Ya Turnuƙe APC A Kano
- Horon Da Muka Samu A Kasar Amurika Zai Yi Tasiri Wajen Magance Fadan Daba: SP Abdullahi H Kiyawa
Kayayyakin da aka ƙwato daga wurin sun haɗa da: bindigogi ƙirar AK-47 ɗauke da harsasai da Babura da rediyon Baofeng da wayoyin salula da magungunan kashe ƙwayoyin cuta da magunguna na ruwa da ƙananan na’urorin masu tara hasken rana, waɗanda ake kyautata zaton ’yan ta’addan na amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
Sojojin sun ci gaba da bibiyar ’yan ta’addan da suka tsere a wani mataki na ci gaba da kai hare-hare a yankin baki ɗaya.
