Home » Sojojin Najeriya sun yi arangama da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP

Sojojin Najeriya sun yi arangama da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP

by Anas Dansalma
0 comment
Sojojin Najeriya sun yi arangama da 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP

Sojojin Najeriya da ke rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai sun harbe wasu ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP da ke kokarin tsallakowa Najeriya daga Jamhuriyar Kamaru.

Yan ta’addan, wadanda suka kai biyar dai, a cewar sojoji sun kwashi kashinsu a hannu ne sakamakon wasu bayanan sirri da aka samu.

Sabon Daraktan Yada Labarai na Hedkwatar Tsaro, Manjo Janar ES Buba, ne ya bayyana haka a hedkwatar tsaro da ke Abuja, ranar Alhamis.

Ya ce sun yi wa ’yan ta’addan kwanton bauna ne a kan hanyar Bula, Yobe zuwa Darel Jamel a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.

Ya kuma ce dakarun sun sami nasarar cafke wasu ’yan ta’addan su 10 da ransu.

Buba, wanda mataimakinsa, Birgediya Janar Abdullahi Ibrahim ya wakilta, ya ce sun kuma kama makamai masu yawa daga hannun ’yan ta’ddan.

Daga cikin kayayyakin ya ce har da buhun fulawa  da na omo, sannan kuma an kama masu hada baki da su.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?