Jim kadan bayan saukar sabuwar manhajar Threads da zafinta, ‘yan Nijeriya sun kasance a gaba-gaba wajen yin maraba da wannan dandali.
A ranar Alhamis ne kamfanin Meta mamallakin Facebook da Instagram da WhatsApp ya kaddamar da Thread, wata manhaja da ta kasance tamkar kishiya ga Twitter saboda kamanceceniyarsu.