• Home  
  • Sojojin Nijeriya Sun Kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Kachalla Kallamu
- Babban Labari - Labarai

Sojojin Nijeriya Sun Kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Kachalla Kallamu

Sojojin Najeriya sun ce sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Kallamu, wanda na hannun damar Turji ne a ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto. Jaridar Daily Trust mai zaman kanta ce ta ruwaito daga wata majiya cewa an kashe ɗanbindigar ne a ranar Laraba, inda ta ce an samu nasarar kashe Kallamu ne […]

Sojojin Najeriya sun ce sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Kallamu, wanda na hannun damar Turji ne a ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.

Jaridar Daily Trust mai zaman kanta ce ta ruwaito daga wata majiya cewa an kashe ɗanbindigar ne a ranar Laraba, inda ta ce an samu nasarar kashe Kallamu ne tare da taimakon ƴan sa kai.

Kallamu ɗan asalin garin Garin-Idi ne da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni, inda rahotanni suka ce Kallamu ya tsira daga wasu hare-haren sojoji a baya, inda aka ce ya tsere zuwa jihar Kogi.

Jihar Sokoto ta daɗe tana fama da matsalolin tsaro, duk da irin nasarorin da sojojin Najeriya suke cewa suna samu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai