• Home  
  • Sunayen sabbin shugabannin jam’iyar APC
- Babban Labari

Sunayen sabbin shugabannin jam’iyar APC

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zaɓi sabbin shugabannin da za su jagorance har an da shekaru huɗu masu zuwa. An zaɓi sabbin shugabbnin ne a lokacin babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar ranar Juma’a a Abuja. APC ta sanar da zaɓen Farfesa Nentawe Yilwatda – shugaban riƙon jam’iyyar – a matsayin cikakken […]

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zaɓi sabbin shugabannin da za su jagorance har an da shekaru huɗu masu zuwa.

An zaɓi sabbin shugabbnin ne a lokacin babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar ranar Juma’a a Abuja.

APC ta sanar da zaɓen Farfesa Nentawe Yilwatda – shugaban riƙon jam’iyyar – a matsayin cikakken shugabanta na ƙasa.

Haka kuma jam’iyyar ta tabbatar da Surajudeen Basiru a matsayin cikakken sakataren jam’iyyar na ƙasa.

An dai zaɓi mafi yawan jagororin jam’iyyar ta hanyar masalaha, kamar yadda jam’iyyar ta fi bai wa fifiko.

Ga jerin sunayen sabbin jagororin jam’iyyar:

  • Shugaban Jam’iyya na ƙasa: Farfesa Nentawe Yilwatda
  • Mataimakin Shugaba (Arewa): Ali Bukar Dalori
  • Mataimakin Shugaba (Kudu): Dr. Benjamin Obi Nwoye
  • Sakataren Jam’iyyar na ƙasa: Sen. Surajudeen Ajibola Basiru
  • Mataimakin Sakatare: Prof. AbdulKarim Abubakar Kana
  • Babban Lauyan Jam’iyya: Murtala Aliyu Kankia
  • Babban Ma’aji na ƙasa: Uguru Mathew Ofoke
  • Babban Sakataren Kuɗi: Amb. Haruna Ginsau
  • Babban Sakataren tsare-tsare: Muhammad Sulaiman Argungu, OFR
  • Sakataren Walwawa: Donatus Enyinnah Nwankpa
  • Sakataren Yaɗa Labarai: Felix Morka
  • Babban Mai Binciken kuɗi: Sen. Abubakar Maikafi
  • Shugabar Mata: Dr Mary A. Idele
  • Shugaban Matasa: Dayo Israel

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai