ECOWAS ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa Guinea
Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta amince da ɗage dukkan sauran takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasar Guinea bayan kammala miƙa mulki, lamarin da ke nuna cikakken dawowar ƙasar cikin harkokin ƙungiyar yankin. An cimma wannan matsaya ne a yayin taron shugabannin ƙasashe da gwamnatocin ECOWAS da aka gudanar a ƙasar […]