Ecowas Ta Yi Watsi Da Iƙirarin Trump Na Kisan Kiristoci A Najeriya

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, Ecowas ta yi watsi da abin da ta kira iƙirarin ƙarya mai cike da hatsari da shugaban Amurka ya yi cewa ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na far wa kiristoci tare da kashe su a Najeriya.

Matakin na zuwa ne bayan da Shugaba Trump na Amurka ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, kana bin da ya bayyana da kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a ƙasar.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Talata ta ce irin wannan na Shugaba Trump ka iya ta’azzara matsalar tsaro tare da haifar da matsalar zamantakewa a yankin da dama ke fama da matsalar masu tsattsauran ra’ayi.

Ecowas ta jaddada cewa hare-haren masu tsattsauran ra’ayi a yankin Afirka ta Yamma na shafar mutanen da ba su ji ba su gani ba, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ko jinsi ba.

Kan haka ne kungiyar ta buƙaci ƙasashen duniya su tallafa wa kowace ƙasa wajen yaƙi da ta’addanci da ke shafar kowa da kowa.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda