Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta amince da ɗage dukkan sauran takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasar Guinea bayan kammala miƙa mulki, lamarin da ke nuna cikakken dawowar ƙasar cikin harkokin ƙungiyar yankin.
An cimma wannan matsaya ne a yayin taron shugabannin ƙasashe da gwamnatocin ECOWAS da aka gudanar a ƙasar Saliyo, bayan kammala miƙa mulkin siyasa a ƙasar, kamar yadda gidan jaridar Africaguinee mai zaman kanta ta ruwaito.
ECOWAS ta bayyana cewa an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 28 ga Disamba, 2025, kuma an miƙa mulki bisa doka ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Mamadi Doumbouya.
A cewar rahoton, shugabannin yankin sun lura cewa wannan miƙa mulki ya samar da yanayi mai kyau na dawo da dimokuraɗiyya da mutunta doka da oda a Guinea.
ECOWAS ta taɓa dakatar da Guinea tare da ƙaƙaba mata takunkumi ne bayan juyin mulkin da aka yi a 2021, wanda Mamadi Doumbouya, a wancan lokaci soji, ya jagoranta, inda aka kifar da tsohon shugaban ƙasa Alpha Condé.