Labarai
Yan Sandan Kano Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Mutane, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Dajin Falgore.
Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da hannu a sace Alhaji Kabiru Aliyu a ƙauyen Falgore da ke ƙaramar hukumar Doguwa, tare da ƙwato bindigar AK-47 da alburusai 18 a dajin Falgore. Sanarwar da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta ce an kama wanda ake zargin […]

