• Home  
  • Iyalan jami’an yan sanda 17 sun samu tallafin Naira miliyan 7.5 a Kano.
- Labarai

Iyalan jami’an yan sanda 17 sun samu tallafin Naira miliyan 7.5 a Kano.

  Rundunar yan sandan jihar Kano ta bai wa iyalan jami’anta 17 da suka mutu a bakin aiki kuɗi sama da naira miliyan 7.5, a wani ɓangare na shirin tallafa wa iyalan jami’an da suka rasu. Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya miƙa cak ɗin ga waɗanda suka amfana a hedikwatar […]

 

Rundunar yan sandan jihar Kano ta bai wa iyalan jami’anta 17 da suka mutu a bakin aiki kuɗi sama da naira miliyan 7.5, a wani ɓangare na shirin tallafa wa iyalan jami’an da suka rasu.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya miƙa cak ɗin ga waɗanda suka amfana a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano, ranar Litinin.

Jimillar kuɗin da aka raba ta kai naira miliyan 7 da dubu 573 da ɗari 231 da kobo 83, ƙarƙashin tsarin inshorar rayuwa na rundunar, wanda ke cikin shirye-shiryen walwalar jami’an ’yan sanda.

CP Bakori ya ce tallafin wani mataki ne na nuna cewa rundunar ba za ta manta da sadaukarwar jami’an da suka rasa rayukansu wajen gudanar da aikinsu ba.

Ya kuma buƙaci iyalan da suka amfana su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata, tare da tabbatar musu cewa ƙofar ofishinsa a buɗe take domin taimaka musu idan buƙata ta taso.

A madadin waɗanda suka amfana, ASP Ado Sule mai ritaya, wanda ya karɓi cak a madadin matarsa da ta rasu tana aikin ɗan sanda, ya gode wa Sufeto-Janar na ’yan sanda da kwamishinan rundunar Kano bisa tallafin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai