Nigeria

Ya Kamata A Ba NJC Ikon Naɗa Shugaban INEC

A Najeriya yayin da zaɓen 2027 ke matsowa kusa wasu sun fara yin kiran karɓe ikon naɗa shugaban hukumar zaɓen ƙasar watau INEC daga hannun shugaban ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada. Masu irin wannan ra’ayi na ganin cewa hakan na kawo cikas ga ingancin zaɓen ƙasar, a don haka ya kamata […]

Read more

Ganduje Ya Yi Murabus Daga Shugabancin Jam’iyyar APC

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar. Murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take. Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya bayyana rashin lafiya a matsayin dalilin da ya da ya ajiye muƙaminsa. Ganduje ya zama Shugaban APC a watan Agustan 2023, a lokacin da jam’iyyar […]

Read more

Mijina Bai Saci Kuɗin Nijeriya Ba: Maryam Abacha

  Uwargidan tsohon shugaban Nijeriya, Maryam Abacha ta musanta zarge-zargen da ake yi wa mijinta na wawure maƙudan kuɗaɗen ƙasar a lokacin da yake kan karagar mulki. A wata hira da aka yi da ita a kafar talabijin ta TVC a yayin cika shekara 27 da rasuwar Abacha, Maryam ta nanata cewa bai sace kuɗaɗen […]

Read more

Tinubu Ya Karrama Bill Gates Da Lambar Yabo Ta CFR

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya karrama ɗaya daga cikin hamshaƙan attajiran duniya, Bill Gates da lambar yabo ta CFR. An yi bikin karrama attajirin ne ranar Talata a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar. Attajirin shi ne mai fitaccen kamfanin fasahar nan na Microsoft da kuma gidauniyar Bill Gates. A watan da ya […]

Read more

NDLEA Ta Kama Maniyyata Aikin Hajji Dauke Da Hodar Iblis

Shugaban Hukumar da ke yaƙi da shan miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA Janar Buba Marwa (mai ritaya), a ranar Laraba, ya bayyana kamen wasu mutum biyu da suka yi yunƙurin safarar hodar Iblis a lokacin da ake jigilar maniyyata aikin hajji a kan hanyarsu ta zuwa ƙasar Saudiyya don gudanar da Hajjin bana. Da yake […]

Read more

Gwamnatin Tinubu Ba Ta Tausayin Ƴan Najeriya – Atiku Abubakar

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kakkausar murya, yana mai cewa cikin shekara biyu kacal, gwamnatin ta nuna gazawa, kuma gwamnati ce wadda ba ta tare da jama’a sannan maras jin tausayin talakawa fiye da kowacce gwamnati tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya […]

Read more