NDLEA Ta Kama Maniyyata Aikin Hajji Dauke Da Hodar Iblis

Shugaban Hukumar da ke yaƙi da shan miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA Janar Buba Marwa (mai ritaya), a ranar Laraba, ya bayyana kamen wasu mutum biyu da suka yi yunƙurin safarar hodar Iblis a lokacin da ake jigilar maniyyata aikin hajji a kan hanyarsu ta zuwa ƙasar Saudiyya don gudanar da Hajjin bana.

Da yake jawabi a wajen buɗe taron kwamitin kula da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Abuja, Marwa ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin sun haɗiyi miyagun ƙwayoyin ne, inda suka nuna cewa su Musulmi ne masu kishin addini da suke shirin gudanar da aikin hajji.

“Kwanaki kaɗan da suka wuce, mun kama wasu maniyyata biyu da za su je ƙasar Saudiyya aikin Hajji, inda suka haɗiye hodar iblis, suna nuna cewa za su je ƙasar ne don yin hajjin bana,” in ji shi.

Shugaban Hukumar ta NDLEA ya bayyana damuwarsa kan yadda rukuni masu aikata laifuka ke ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙasashen duniya musamman a lokacin aikin Hajji.

Shekaru biyu da suka wuce, an damfari mata uku. Wasu mutane sun yi tayin biyan tikitin su, da biza da sauransu. Kafin su tafi an ba su wata ’yar ƙaramar jaka don kai wa wani da ake zaton ɗan uwa ne a ƙasar Saudiyya. Ba su san shi ba, an ɗinke hodar iblis ɗin a cikin jaka,” in ji shi.

Marwa ya lura cewa, duk da ƙalubalen kuɗaɗe da suka shafi cikakken aiwatar da babban tsarin hana shan muggan ƙwayoyi na ƙasa (2021-2025), hukumar ta ci gaba da jajircewa kan manufar ayyukanta.

Post masu alaƙa

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda

‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto