Labarai
Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 daga masu garkuwa a Kogi.
Sojojin Najeriya sun ceto mutane tara, ciki har da jariri, bayan arangama da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kan hanyar Ajaokuta zuwa Itobe a Jihar Kogi. Dakarun Bataliya ta 21 sun bi sawun masu garkuwar har zuwa kusa da Adumu, inda suka yi musu luguden wuta, lamarin da ya tilasta […]

