YAN BINDIGA

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

Rahotanni daga yankin Ƙaramar Hukumar Matazu da ke Jihar Katsina sun ce jami’an tsaro sun kashe wasu manyan kwamandojin ’yan bindiga biyu a wani artabu da suka yi da ’yan ta’addan da ke ƙarƙashin jagorancin wani da ake kira Kachalla Fulani. Majiyoyi sun ce artabun ya biyo bayan wani harin kwanton ɓauna da ’yan bindigar […]

Read more

An Ceto Daliban Da Yan Bindiga Suka Sace A Kebbi

Hukumomin Najeriya sun sanar da kuɓutar da ɗaliban Sakandiren ƴan mata da ke garin Maga a jihar Kebbi su 24. Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya yi wa ɗaliban maraba da dawowa. Shugaba Tinibu ya kuma ya yaba wa ƙoƙorin jami’an […]

Read more

An Kama Yan Bindiga 5 A Jihar Kebbi

’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu ’yan bindiga biyar tare da ƙwace tarin makamai a hannunsu a yankin Zuru–Tadurga da ke Jihar Kebbi. Rundunar ’yan sanda ta musamman da ta kama su, ta bayyana cewa, ’yan bindiga suna cikin waɗanda suka kai hare-hare a kan al’ummomin Zuru a kwanakin baya. Ta ƙara da cewa […]

Read more

Yan Bindiga Sun Sace Mata 5 A Kano

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari garin Ƴankwaɗa da ke Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata shida ciki har da masu shayarwa, tare da harbin mutum ɗaya. Wannan na zuwa ne mako guda bayan kai irin wannan harin a wasu kauyuka a ƙananan hukumomin […]

Read more

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 5 A Masallaci A Zamfara

Aƙalla mutum biyar ne suka rasu lokacin da ’yan bindiga suka kai hari wani Masallaci,  yayin da ake tsaka da sallar Asuba a garin Yandoto da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin Masallacin inda suka fara harbi ba tare da ƙaƙƙautawa ba, inda suka kashe mutum biyar […]

Read more