Sojojin Operation Haɗin Kai sun kashe ‘yan tada ƙayar baya daga tsaunukan Mandara a lokacin wani yunƙurin da suka yi da tsakar dare don kai hari cikin al’ummar Bitta da ke Borno.
Majiyoyin tsaro sun shaida cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na daren wayewar ranar Alhamis lokacin da sojoji, waɗanda ke aiki tare da sa ido, suka gano wannan yunƙuri na ‘yan ta’addar da ke tafiya zuwa yankin.
A cewar majiyoyin, sojojin sun yi wa ’yan ta’addan ƙofar rago yadda suka shiga wani yanki da aka musu tarko kafin su buɗe musu wuta, inda suka kashe wasu daga cikin maharan, ciki har da wani babban mayaƙin ’yan ta’adda da mai ɗaukar musu hoto.
Majiyoyin sun ƙara da cewa, daga baya rundunar sojojin sama ta Operation Haɗin Kai ta kai farmaki da suka biyo baya, wanda suka ƙara kashe ‘yan ta’addan da suka gudu don tsira.
Abubuwan da aka gano daga wurin sun haɗa da: Na’urar ɗaukar hoto, bindigogin AK-47, rediyon hannu, bindigogin samfurin PKT, bel da harsasai masu alaƙa da GPMG da kuma babura da kekuna.
A lokacin da ake fafatawa a yankin, an ruwaito cewa sojoji sun bi diddigin hanyoyi da dama, kuma sun gano kaburbura marasa zurfi, wanda ke nuna ƙarin asarar rayuka da aka yi wa ‘yan ta’addan a lokacin fafatawar.