Yan Bindiga Sun Kashe Mai Juna Biyu Da Wasu Mutane 4 A Sokoto

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin.

“Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su yi garkuwa da su. A wasu lokuta ma suna ɗora wa al’umma haraji, idan ba a biya cikin wa’adin da suka bayar ba, sai su kawo hari,” in ji shi.

Wata majiya ta bayyana cewa akwai wasu mutum biyu da suka jikkata sakamakon harbin bindiga da ke karɓar magani a wani asibiti da ke kusa da yankin.

Shugaban al’umma a yankin ya roƙi gwamnati ta kafa ofishin jami’an tsaro a yankin domin daƙile barazanar maharan, yana mai cewa yanzu babu ko ɗaya a yankin.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce bai samu rahoton lamarin ba tukuna, amma zai bincika.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, bai waiwayi Aminiya da wani ƙarin bayani ba.

Ƙauyen Alkalije na cikin gundumar Kilgori da ke iyaka da Ƙaramar Hukumar Silame da wasu ƙauyuka na Jihar Kebbi.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda