An Kama Yan Bindiga 5 A Jihar Kebbi

’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu ’yan bindiga biyar tare da ƙwace tarin makamai a hannunsu a yankin Zuru–Tadurga da ke Jihar Kebbi.

Rundunar ’yan sanda ta musamman da ta kama su, ta bayyana cewa, ’yan bindiga suna cikin waɗanda suka kai hare-hare a kan al’ummomin Zuru a kwanakin baya.

Ta ƙara da cewa dukkansu ’yan asalin kauyen Birnin Tudu ne da ke cikin ƙananan hukumomin Bukkuyum da Gummi a Jihar Zamfara.

Kakakin ’yan sanda a jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce makaman da aka ƙwato daga hannun ’yan bindigar sun haɗa bindigogi AK-47 guda 7 a wata ƙaramar gida guda 1 da harbi-ruga guda uku.

Post masu alaƙa

JIGAWA: ‘Yan siyasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben 2027

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.