Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Maryam Sanda wadda ke zaman jiran hukuncin kisa bisa samun ta da laifin kashe maigidanta.
Wannan na ɗauke a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Tinubu kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.
A farkon watan Oktoba nan ne dai shugaba Tinubu ya yi wa wasu mutum 175 afuwa da suka haɗa da matattu da masu rai.
Sai dai kuma shugaban ya fuskanci suka daga ɓangarori da dama na ƙasar, wani abun da ake ganin shi ya sa gwamnatin ta fito ta ce za ta sake waiwayar jerin sunayen.
A jerin sunayen na farko da aka fitar, ya ƙunshi mutum 175 ciki har da Maryam Sanda wadda aka yi ta sa-in-sa dangane da yi mata afuwar.
To sai dai sabon jerin sunayen mutanen ya ƙunshi mutum 34 ne kawai, inda aka kasa su gida uku waɗanda aka yi wa afuwa da waɗanda mayar da hukuncin kisar da aka yi musu zuwa ɗaurin rai da rai da kuma waɗanda aka yi afuwa amma ba tare da yafe musu laifin nasu ba.
Su ne mutum 15 da aka yafewa laifin da suka yi sannan kuma aka wanke su daga laifin wanda hakan ke nufin ba za a taɓa alaƙanta su da laifin ba sannan idan akwai wasu haƙƙoƙinsu da aka hana su sakamakon aikata laifin to yanzu za a ba su haƙƙoƙin nasu.
Mrs Anastasia Daniel Nwaobia
Barrister Hussaini Alhaji Umar
Ayinla Saadu Alanamu
Hon Farouk Lawan
Herbert Macaulay
Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa
Ken Saro Wiwa
Saturday Dobee
Nordu Eawo
Daniel Gbooko
Paul Levera
Felix Nuale
Baribor Bera
Barinem Kiobel
John Kpuine
Daga hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai
Wannan jerin sunayen mutum huɗu ne waɗanda aka rage girman hukuncin da aka yanek musu sakamakon laifin da suka aikata, inda aka rage hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai.
Emmanuel Baba
Abubakar Usman
Khalifa Umar
Mohammed Umar
Waɗanda aka yafewa amma tabon zai bi su
Oroka Michael Chibueze
Adesanya Olufemi Paul
Daniel Bodunwa
Hamza Abubakar
Buhari Sani
Mohammed Musa
Maharazu Abubakar
Ibrahim Yusuf
Saad Ahmed Madaki
Kofur Michael Bawa
Richard Ayuba
Adam Abubakar
Emmanuel Yusuf
Chinedu Stanley
Johny Ntheru Udor.
Sanarwar da Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ta ce shugaba Tinubu ya sake waiwayar jerin sunayen mutanen da aka yi wa afuwar ne sakamakon tuntuɓar Majalsiar Ƙasa da kuma ra’ayoyin ƴan Najeriya kan batun.
“Shugaban ƙasa ya yi umarnin a sake bibiyar da waiwayen jerin sunayen waɗanda aka yi wa afuwar da farko…inda aka goge sunayen mutanen da suka aikata manyan laifuka kamar garkuwa da mutane da safarar ƙwaya da safarar bil’adama da damfara da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba….sannan kuma aka rage hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai ga wasu waɗanda aka yafewa a farko.”
Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaukar matakin ya zama dole ne bisa la’akari da girman laifukan da alaƙarsu da matsalar tsaro da ƙasar ke ciki da kuma nuna damuwa da halin da ƴan uwa da iyalan wadanda masu laifin suka saɓawa
“Shi adalci abu ne mai fuska uku – Wanda ya aikata laifi da wanda aka yi wa laifin da kuma ƙasa ko kuma al’umma saboda haka ne ma aka yi wani waiwayen,” in ji sanarwar.

