Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi wata kotu a Amurka ta hana Ma’aikatar Shari’a ta Amurka (DOJ) da hukumomin FBI da DEA fitar da wasu takardunsa da ake dangantawa da zargin safarar miyagun ƙwayoyi da aka taɓa yi masa, a cewar lauyoyinsa.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Tinubu ya shigar da ƙorafi ne a wani shari’ar neman bayanai da wani ɗan gwagwarmayar neman gaskiya a Amurka, Aaron Greenspan, ya buɗe ƙarƙashin dokar ’Yancin Samun Bayanai (FOIA).
Greenspan na neman a ba shi cikakken fayil ɗin FBI da sauran bayanan binciken da suka shafi Tinubu, ciki har da wasu bayanan da suka danganci shari’ar kwace kusan dala 460,000 a Amurka a shekarar 1993.
Sai dai lauyoyin Tinubu sun ce fitar da waɗannan takardu na iya ƙeta haƙƙinsa na sirri, suna masu cewa ko da an taɓa bayyana wasu bayanai a baya, har yanzu yana da haƙƙin kare bayanan da ba a fitar da su ba.
Tinubu dai ya sha musanta aikata wani laifi da ya shafi zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
