Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi sababbin hafsoshin tsaron ƙasar su zage damtse domin magance sababbin barazanar tsaro da ke kunnowa.
Da yake magana bayan bikin ƙara wa shugabannin rundunonin soji girma yau Alhamis a Abuja, Tinubu ya ce: “Barazanar tsaro na ƙara sauyawa a kodayaushe, kuma abin da ya fi damun gwamnatinmu shi ne ɓullar sababbin ƙungiyoyin ‘yanbindiga a arewa ta tsakiya, da arewa maso yamma, da wasu yankunan kudanci.”
A jiya Laraba ne majalisar dattawa da ta wakilai suka amince da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan tsaro, da Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin hafsan sojan ƙasa, da Rear Admiral Idi Abbas hafsan sojan ruwa, da Air Marshall Kennedy Aneke hafsan sojan sama, da Manjo Janar Emmanuel Undiendeye shugaban tattara bayanan sirri na soja.
“Ba zai yiwu mu ƙyale wannan sabuwar barazanar ta ci gaba ba. Dole ne mu ɗauki mataki da wuri. Mu sare kan macijin,” in ji Tinubu.
Yayin bikin an ƙara wa Olufemi Oluyede muƙami zuwa janar, Waidi Shaibu zuwa laftanar janar, Idi Abbas zuwa Vice Admiral, da Kevin Aneke zuwa air vice marshall, da kuma Emmanuel Undiendeye zuwa laftanar janar.

