• Home  
  • Tinubu ya rantsar da mai riƙon muƙamin gwamnan jihar Rivers
- Babban Labari

Tinubu ya rantsar da mai riƙon muƙamin gwamnan jihar Rivers

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, mai ritaya a matsayin gwamnan riƙo na jihar Rivers, bayan ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar, jiya Talata. Bukin rantsuwar ya gudana ne yau Laraba a fadar shugaban Najeriyar da ke Abuja. A ranar Talatar ne Tinubu ya sanar da sunan Ibas a matsayin […]

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, mai ritaya a matsayin gwamnan riƙo na jihar Rivers, bayan ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a jihar, jiya Talata.

Bukin rantsuwar ya gudana ne yau Laraba a fadar shugaban Najeriyar da ke Abuja.

A ranar Talatar ne Tinubu ya sanar da sunan Ibas a matsayin wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar ta Rivers, bayan dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba wa jihar, lamarin da ke nufin an dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa da kuma ƴanmajalisar dokokin jihar na tsawon wata shida.

Jihar Rivers ta kwashe tsawon lokaci cikin rikita-rikitar siyasa, lamarin da ya kai ga yunƙurin tsige gwamnan jihar da kuma rushe zauren majalisar dokokin jihar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai