• Home  
  • Tsohon mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam ya fice daga NNPP
- Babban Labari

Tsohon mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam ya fice daga NNPP

A hukumance, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya fice daga jam’iyyar NNPP. Gwarzo ya sanar da ficewar tasa ne cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar NNPP na mazaɓarsa ta Gwarzo, inda ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne sakamakon sabbin sauye-sauyen siyasa da ke faruwa a jihar Kano. […]

A hukumance, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya fice daga jam’iyyar NNPP.
Gwarzo ya sanar da ficewar tasa ne cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar NNPP na mazaɓarsa ta Gwarzo, inda ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne sakamakon sabbin sauye-sauyen siyasa da ke faruwa a jihar Kano.
Ya ce matakin na sa ya biyo bayan bukatar ci gaba da laluben hanyoyin bunkasa dimokaradiyya da kuma kara taimakawa al’umma a Kano da ma kasa baki ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na Gwarzo na zuwa ne awanni kadan bayan da jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya fara shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar, tare da alakanta hakan da yiwuwar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC.
Lamarin na kara nuna yadda siyasar jihar Kano ke ci gaba da sauyawa yayin da manyan jiga-jigan jam’iyya ke daukar sababbin matakai.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai