Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Alkalai na Najeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Mohammed, rasuwa.
Mai Shari’a Ibrahim Tanko Mohammed, ya rasu yana da shekara 71, kamar yadda Gwamnatin Jihar Bauchi ta tabbatar.
Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke kasar Saudiyya a ranar Talata da safe.
Kungiyar Dalibai Musulmi a Fannin Aikin Lauya ta Najeriya (NAMLAS) ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin.
- Tsohon shugaban kasa Buhari Mutum ne mai ladabi da kishin kasa- Bola Tinubu
- Jiragen soji sun yi raga-raga da rumbun makaman Boko Haram a Borno
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta bayyana rasuwar Mai Shari’a Tanko Mohammed a matsayin “babban rashi ga fannin aikin shari’a a Najeriya, daukacin aikin shari’ar, da al’ummar Musulmi baki daya.”
Hakazalika Gwamantin Jihar Bauchi ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, tana mai addu’ar Allah Ya yi masa rahama, Ya kuma ba wa iyalansa hakurin jure wannan rashi.
