Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi uku na tsawon watanni uku bisa zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati da amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba.
Ciyamomin da aka dakatar su ne Bello Abdullahi Gadanya na Bagwai, Alhassan Salisu na Bebeji da Abubakar Mustapha na Rogo.
Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Majalisar, wanda shugabansa, Aliyu Muhammad, ya gabatar a zaman majalisar da kakakin majalisar, Ismail Falgore, ya jagoranta.
Rahoton kwamitin ya ce an samu zargin karkatar da kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa a Ƙaramar Hukumar Bagwai.
A Bebeji kuwa, kwamitin ya ce ya gano zarge-zargen amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba, take dokokin bayar da kwangila da aiwatar da su, sayar da filayen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba da karkatar da kuɗaɗen jama’a.
Rahoton ya kuma zargi shugaban ƙaramar hukumar Bebeji da tilasta wa ‘yan kwangila tura kuɗaɗen kwangilarsu zuwa wasu asusun banki da ake zargin shi ne ya zaɓa.
A Rogo kuma, kwamitin ya ce shugaban ƙaramar hukumar na fuskantar zargin yin karan tsaye ga manufofin gwamnati, amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba da kuma karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan gina hanyoyin karkara da samar da wutar lantarki a al’ummomin Unguwar Dawa da Hausawa Fulani.
Kwamitin ya ba da shawarar dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin har sai an kammala cikakken bincike, yana mai kafa hujja da sashe na 128 da 129 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999.
