Rundunar yan sandan jihar Kano, ta shirya domin wayar da kan jama’a, kan tukin ababen hawa da kuma tabbatar da doka.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa,ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.
Rundunar ta ce ta yi kiran ne sakamakon abubuwan da suke faruwa, inda wasu daga cikin mutane ke karya dokokin tuki ta hanyar bin hannu daya, kin tsaya adaidai lokacin da fitilar bayar da hannu ta tsayar da mutum da kuma sauran laifuka dabam-daban wadanda ake atikata su da ke janyo haduran ababen hawa da cunkoso a wasu sassan Kano.
Haka zalika rundunar ta yabawa gwamnatin jihar Kano, musamman na sabunta Tituna da yin sababbi, Inda rundunar ta yi kira ga jama’a da su yi godiya da kuma yin biyayya lokacin da ake tuki kan wandanan Titunan .
CSP Abdullahi Haruna, ya kara da cewa shirin wayar da kan zai magance yin tukin mota ba tare da Lamba ba ko kuma wadda aka tufe ko bin hannu daya da wadanda basa tsayawa fitulun titi ko wata alama da aka saka da masu gudun wuce Sa’a da tukin ganganci.
Rundunar ta ce za a magance masu shan miyagun kwayoyi yayin tuki da masu yin amfani da waya ko yin fakin ba bisa ka’ida ba, da yin lodin da wuce kima ko masu tare hanyar al’umma.
Sanarwar ta yi kira ga jama’a, da su yi amfani da wannan gargadi domin bin dokokin tuki, kuma bayan an kammala wayar da kan za a yi aikin tabbatar da tsaro kuma duk wanda aka kama da laifin karya dokar tuki za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano,CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar zata ci gaba da zage dantse domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya na jihar baki daya.
Sannan rundunar ta ce wannan jajircewa umarnin babban sufeton yan sandan jihar Kano, IGP Olatunji Rilwan Disu, ne wanda ya bayar domin yon aikin tsaro da al’umma da tattara bayanan sirri da yin aiki da na’urorin zamani domin tabbatar da tsaro da daukar matakan da suka kamata domin a zauna lafiya.
A karshe rundunar ta nemo hadin kan al’umma musamman, kungiyar NATO , kungiyar NURTW, iyayen kasa, Malamai, Yan jarida da kuma sauran shugabannin kowanne bangare domin tsabtace Tituna da tsaro.
