Home » UNICEF Ta Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Su Samar Da Shirye-shiryen Bunƙasa Rayuwar Yara

UNICEF Ta Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Su Samar Da Shirye-shiryen Bunƙasa Rayuwar Yara

by Anas Dansalma
0 comment

Asussun Tallafawa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na gudanar da taron wayar dai kai na kwana biyu da wakilan kafafan yada labarai na jahohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna da nufin samar da hanyoyin karfafa muryar yara domin mahukunta su ɗau matakan kulawa da kuma kare haƙƙoƙinsu.

Jami’in hulɗa da Jama’a na UNICEF mai kula da jahohin Kano da Jigawa da Katsina, Mr. Samuel Kaalu ya ce maƙasudin taron shi ne jan hankulan kafafa yaɗa labarai wajen bai wa buƙatun yara muhimmanci a kafofinsu da kuma fito da matsalolin da yara ke fuskanta a waɗannan jahohi da nufin magance su.

Mr. Samuel Kaalu ya yaba da irin gudunmawar da kafafan yaɗa labarai ke bayarwa wajen ganin Asusun Tallafa wa Ƙananan Yara (UNICEF) ta cimma manufofinta.

Wasu daga cikin Gidajen yada labarai da suka halarci taron su hada da: gidan Rediyon Kano da Muhasa da Aminci rediyo da Arewa da Legend FM Daura da gidan talbija na NTA Kano da na Katsina da gidan jaridar Punch.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?