• Home  
  • UNICEF Ta Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Su Samar Da Shirye-shiryen Bunƙasa Rayuwar Yara
- Babban Labari - Labarai

UNICEF Ta Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Su Samar Da Shirye-shiryen Bunƙasa Rayuwar Yara

Asussun Tallafawa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na gudanar da taron wayar dai kai na kwana biyu da wakilan kafafan yada labarai na jahohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna da nufin samar da hanyoyin karfafa muryar yara domin mahukunta su ɗau matakan […]

Asussun Tallafawa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na gudanar da taron wayar dai kai na kwana biyu da wakilan kafafan yada labarai na jahohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna da nufin samar da hanyoyin karfafa muryar yara domin mahukunta su ɗau matakan kulawa da kuma kare haƙƙoƙinsu.

Jami’in hulɗa da Jama’a na UNICEF mai kula da jahohin Kano da Jigawa da Katsina, Mr. Samuel Kaalu ya ce maƙasudin taron shi ne jan hankulan kafafa yaɗa labarai wajen bai wa buƙatun yara muhimmanci a kafofinsu da kuma fito da matsalolin da yara ke fuskanta a waɗannan jahohi da nufin magance su.

Mr. Samuel Kaalu ya yaba da irin gudunmawar da kafafan yaɗa labarai ke bayarwa wajen ganin Asusun Tallafa wa Ƙananan Yara (UNICEF) ta cimma manufofinta.

Wasu daga cikin Gidajen yada labarai da suka halarci taron su hada da: gidan Rediyon Kano da Muhasa da Aminci rediyo da Arewa da Legend FM Daura da gidan talbija na NTA Kano da na Katsina da gidan jaridar Punch.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai