UNICEF Zai Ba Najeriya kwalabe Miliyan 3 Na Maganin Inganta Lafiyar Masu Ciki

Asusun Tallafawa Yara Kanana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa za ta baiwa Najeriya gudunmawar kwalabe miliyan uku na maganin inganta lafiyar mata masu ciki MMS a bana.

MMS magani ne dake dauke da sinadaran  ‘iron da folic acid’ dake taimakawa wajen inganta lafiyar mace mai ciki da dan dake cikinta.

Maganin na taimakawa wajen kara wa mace mai ciki jini a jikinta tare da kare ta daga haihuwar bakwaini ko jaririn da bashi da koshin lafiya.

Alli-Hakeem ya ce kwalabe miliyan uku din da Asusun za ta bada kari ne kan kwalabe miliyan uku din da Asusun ta fara bada wa a 2024 wanda a yanzu haka Asusun Inganta lafiyar yara kanana CNF ke kula da su.

UNICEF ta ce gidauniyar ‘Kirk Humanitarian’ NE ta fara bada gudunmawar kwalabe miliyan uku a 2024 yayin da ake taron makon inganta lafiyar mata da yara kanana Karo na biyu a shekarar.

Asusun ta Kuma ce a gidauniyar ‘Kirk Humanitarian’ za ta kara bada wasu kwalabe miliyan uku wa gwamnati a cikin wannan shekarar.

Wakilin UNICEF Cristian Munduate ya ce samar wa mata sinadarin da za su taimaka wajen inganta lafiyar su dabara ce da zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mata da inganta lafiyar yara kanana a kasar nan.

Cristian ya ce tallafin maganin MMS da Asusun UNICEF ta bada tabbacin ne na goyan bayan da gwamnatin Najeriya za ta samu daga wajen asusun kan inganta lafiyar mata da yara kanana.

“Burin mu shine mu hada hannu da gwamnatin Najeriya da sauran kungiyoyin bada tallafi domin rage yawan mace-macen mata da yara kanana a Najeriya.

UNICEF ya ce Najeriya na daga cikin kasashen duniyan dake da yawan matan dake mutuwa musamman wajen haihuwa inda a kasar mata 1,047 ne ke mutuwa daga cikin mata 100,000 duk shekara wajen haihuwa.
“Duk shekara akalla mata miliyan 12 ne ke daukan ciki a Najeriya inda gaggauta daukan matakan da za su inganta lafiyar mata da yara ke da mahimmanci.
“Rashin cin abincin dake inganta garkuwar jiki musamman idan har babu sinadarin iron, zinc, Vitamin A na daga cikin matsalolin dake cutar da mace yayin da dake ta ciki.
“Sakamakon binciken da Hukumar Kula da Amfanin Abinci ta Kasa ta gudanar a 2024 ya nuna cewa mata masu ciki da dama a Najeriya na fama da matsalar rashin samun abincin da zai inganta lafiyar su.
“Kawar da matsalolin irin haka zai taimaka wajen inganta lafiyar mata da jarirai a kasar nan.
Ministan lafiya Muhammad Pate ya ce gwamnati na kokari wajen ganin ta farfado da fannin lafiya a kasar nan Yana mai cewa daukan matakin hada wannan maganin a kasar nan zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mata da yara kanana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *