• Home  
  • Yar Najeriya ta kammala jami’ar Burtaniya da daraja ta daya (1st Class) a ilimin kimiyar samar da manhajar kasuwancin zamani.
- Babban Labari

Yar Najeriya ta kammala jami’ar Burtaniya da daraja ta daya (1st Class) a ilimin kimiyar samar da manhajar kasuwancin zamani.

Yar Najeriya, Zainab Muhammad Babandede, ta sake ɗaga martabar ƙasarta, inda ta kammala karatun digirin farko (BSc) a fannin Kimiyyar Samar Da Manhajar Kasuwancin Zamani (Engineering Software for Business) da matsayin Daraja ta Farko (First Class) a Jami’ar University of the West of England (UWE), Bristol, da ke Birtaniya. Wannan gagarumar nasara ta ƙara tabbatar […]

Yar Najeriya, Zainab Muhammad Babandede, ta sake ɗaga martabar ƙasarta, inda ta kammala karatun digirin farko (BSc) a fannin Kimiyyar Samar Da Manhajar Kasuwancin Zamani (Engineering Software for Business) da matsayin Daraja ta Farko (First Class) a Jami’ar University of the West of England (UWE), Bristol, da ke Birtaniya.
Wannan gagarumar nasara ta ƙara tabbatar da cewa matasan Najeriya na ci gaba da nuna bajinta tare da yin fice a manyan jami’o’in duniya, musamman a fannonin kimiyya da fasaha.
Zainab ta samu wannan gagarumar nasara ne bayan ta nuna ƙwazo, jajircewa da ƙwarewa a karatunta, abin da ya sanya ta kasance cikin fitattun ɗaliban da suka kammala wannan karatu cikin nasara.
Ana sa ran wannan nasara za ta zama abin koyi ga matasan Najeriya, musamman mata masu sha’awar shiga fannonin kimiyya, fasaha, da lissafi (STEM).
Jami’ar UWE Bristol na daga cikin fitattun jami’o’in Birtaniya da suka yi suna wajen koyar da darussa masu alaƙa da fasaha, ƙirkire-ƙirkire da bunƙasa ƙwarewar ɗalibai.
Nasarar Zainab ta ƙara nuna irin hazaka da damar da matasan Najeriya ke da ita, ta yin gogayya da kuma yin fice a matakin duniya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000