• Home  
  • An Gano Inda Ake Sabunta Wa’adin Karewar Amfanin Magani A Abia
- Babban Labari - Labarai

An Gano Inda Ake Sabunta Wa’adin Karewar Amfanin Magani A Abia

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta gano wani wuri a Abia da ake sake gyara da sabunta magungunan da suka lalace domin sayar wa jama’a.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta gano wani wuri a Abia da ake sake gyara da sabunta magungunan da suka lalace domin sayar wa jama’a.

NAFDAC ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Hukumar ta ce an gano waɗannan magunguna a wasu gine-gine da ke garin Umumeje, a Ƙaramar Hukumar Osisioma Ngwa.

NAFDAC, ta ce wannan waje yana kusa da kasuwar Ariaria a Aba, cibiyar kasuwanci a jihar.

Hukumar ta bayyana cewa ta kai samame wajen ne tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro domin daƙile safarar jabun magunguna.

Wannan yana ɗaya daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na kare lafiyar al’umma.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai