Home » Kano Da Abuja Sun Sami Tallafin Dabino Tan 100 Daga Saudiyya

Kano Da Abuja Sun Sami Tallafin Dabino Tan 100 Daga Saudiyya

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Gwamnatin Kasar Saudiyya ta bai wa Abuja da Kano tallafin dabino tan 100 domin watan Ramadanan bana.

Ofishin Jakadancin Saudiyya ya gudanar da gagarumin bikin bayar da tallafin dabinon ne a wani ɓangare na ayyukan agaji da yake yi duk shekara.

Shirin da Cibiyar Bayar da Agaji da Jin Ƙai ta Sarki Salman (KSrelief) ta ɗauki nauyin gudanarwa, na da nufin tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi a faɗin ƙasar da kuma ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ƙasashen biyu.

A yayin miƙa tallafin, Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Faisal bin Ibrahim Al-Ghamdi, ya jaddada ƙwazon Masarautar Saudiyya kan ayyukan jin kai.

Ya kuma bayyana matuƙar godiyarsa ga Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud bisa goyon bayan da suke ba wa musulmi da al’ummomi masu rauni a duniya baki ɗaya.

Ya kuma jaddada cewa Saudiyya na nan daram a kan ƙudirin da ta ɗauka na samar da haɗin kan Musulunci da kuma bayar da agaji ga mabuƙata.

Ambasada Al-Ghamdi ya bayyana cewa rabon na bana ya haɗa da tan 50 na dabino na Abuja da kuma wani tan 50 na Kano, a ci gaba da al’adar Saudiyya ta taimaka wa Nijeriya ta hanyar bayar da agaji.

Ya bayyana hakan a matsayin wata babbar manufar Masarautar don ɗaukaka al’ummar Musulmi, rage raɗaɗi, da inganta haɗin kai, musamman a lokuta masu muhimmanci na addini kamar watan Ramadana.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?